Labarai
Kocin Faransa Deschamps zai ajiye aiki bayan Gasar Kofin Duniya ta 2026

Kociyan da ya taimaka wa Faransa lashe gasar Kofin Duniya, Didier Deschamps ya ce zai ajiye aikinsa bayan kammala gasar cin Kofin Duniya ta baɗi da za a gudanar a ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico.
Mai 56, shi ne mutumin da ya fi daɗewa yana jagorantar tawagar ƙasar, bayan da ya fara aikin a 2012.
Ya taimaka wa Faransa lashe gasar Kofin Duniya ta 2018, da aka buga a ƙasar Rasha, sannan ya kai tawagar ƙasar wasan ƙarshe a gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar.
Kafin nan a 2016 ya taimaka wa ƙasar kai wa matakin wasan ƙarshe a gasar nahiyar Turai ta EURO 2016.
“Zuwa 2016, komai zai ƙare. Na cimma burikana,” kamar yadda Deschamps ya shaida wa kafar yaɗa labaran Faransa ta TF1.
“Na cimma muradina, na buri da fatan kai Faransa babban mataki a fagen tamaula”.
Har yanzu Faransa ba ta fara wasanta na neman gurbin Gasar Cin Kofin duniya ta 2026 ba, yayin da rukunin da take ciki ya dogara da sakamakon wasan kwata fayinal da ƙasar za ta kara da Croatia cikin watan Maris.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
