Connect with us

Labarai

Hukumar Fansho Ta Jihar Jigawa Ta Biya Naira Biliyan 1.5 Ga ‘Yan Fansho 609

Published

on

 

 

Hukumar Fansho ta Jihar Jigawa ta biya sama da Naira Biliyan daya da rabi ga mutane 609 da suka yi ritaya daga aiki bayan sun kai shekaru 35 suna aiki, a tsakanin watannin Agusta zuwa Disamban bara.

Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar tallafin aa ofishin ffansho da ke Dutse.

A cewarsa, biyan kudin ya kasu kashi hudu ne, wanda ya nuna cewa kashi na farko na ma’aikata 465 da suka yi ritaya sun kunshi wadanda ko dai sun kai shekaru 35 suna aiki, ko kuma shekara sittin na haihuwa, inda aka biya sama da Naira Biliyan daya miliyan dari 1 da saba’inda uku.

Ya ce, kashi na biyu na ma’aikata 103 su ne wadanda suka mutu a lokacin da suke bakin aiki, inda aka biya magadansu sama da Naira miliyan 315.

Dokta Bilyaminu Shitu ya ci gaba da bayyana cewa, kashi na uku ya kunshi ma’aikata 39 da suka yi ritaya daga aiki kuma suka fara karbar fansho duk wata amma sun mutu kafin su kai wa’adin mafi karancin shekaru biyar bayan ritayar, da aka biya sama da Naira miliyan 54.

Kashi na karshe shi ne wanda ya ci gajiyar tallafin wanda bai kai shekara 5 ba, kuma doka ta bayyana cewa duk ma’aikacin da ya cancanci a biya shi daga tsarin shi ne ya ba da gudummawar na tsawon shekaru biyar. A karkashin wannan fanni, mun biya mutum biyu, kinanin Naira 750, ciki har da kashi 15 bisa dari a matsayin riba“.

Shugaban hukumar ya gargadi ‘yan fansho a fadin jihar da su yi hattara da masu damfara.

Ya kara da cewa, ayyukansu kyauta ne, a don haka ya bukaci masu karbar fansho da jada su ba wani ma’aikaci cin hanci kafin su karbi hakkinsu.

Bilyaminu Shitu ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar da su ci gaba da marawa Gwamnati baya da addu’o’insu, domin ganin an samu Jihar Jigawa mai inganci da kowa zai samu kwanciyar hankali a cikin ajandar ci gaban Jihar.

Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kulawar da yake baiwa ‘yan fansho a jihar.

Biyan fansho da giratuti da aka yi cikin gaggawa ya taimaka wajen kawar da matsin rayuwa ga  ’yan fansho”. Inji shi.

Ya bayyana cewa wannan karimcin zai inganta rayuwa tare da karfafa jin dadin wadanda suka yi ritaya.

Gwamnatin jihar da hukumar za ta ci gaba da tabbatar da biyan fansho cikin gaggawa da sauran hakkokin ma’aikata domin samar da ingantacciyar hidima, jin dadin wadanda suka yi ritaya .”

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar kudaden fanshon, sun yabawa Gwamnan kan yadda ya ba da fifiko kan al’amuran da suka shafi jin dadin ‘yan Fansho.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara