Labarai
Muna Yankin Arewacin Kaduna Ba Kudancin ta ba – Al’ummar Lere
Wadansu Masu kishin Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna sun karyata rade radin dake yawo cewa Lere tana sashin Kuduncin Kaduna ne.
Bayanin haka na kunshe ne a cikin sanarwar da Shugaban gamayyar kungiyoyin Karamar Hukumar Barrista Nasiru Bello Dembo da Sakataren sa Mal. Ahmed Idris suka sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kaduna.
Sanarwar ta bayyana cewa an buga rade radin ne a jaddawalin littafin taron shekara shekara da Kungiyar al’ummar Kudancin Kaduna SOKAPU ta shirya na bana.
Sanarwar tace anga sunaye da hotunan wasu masu rike da mukaman siyasa daga Karamar Hukumar Leren da cewa wakilai ne daga Kudancin Kaduna, lamarin data karyace tsagwaro kuma bashi da tushi balle makama.
A cewar sanarwar wannan ya sabawa sashi na 8 da 48 da kuma 72 na tsarin mulkin Nigeria Wanda ya sanya Lere a mazabar ‘Dan majalisar Dattawa na Arewacin Jihar Kaduna.
Sanarwar ta Kara da cewa Karamar Hukumar Lere bata da wata alaka da sashin Kudancin Kaduna kana ta gargadi wadanda suka shirya taron kada su sake yin haka anan gaba domin gudun Kawo rudami a cikin al’umma.
REL/LERE
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
