Labarai
Jami’an Tsaro Na Samun Nasara Akan Lakurawa a Jihar Kebbi
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne da ba a tantance adadinsu ba, sun kai farmaki ga Alhaji Lawal Black Farm da wasu kauyukan Fulani da ke kusa da kauyen Natsini da ke karamar hukumar Argungu a jihar Kebbi, sun kashe ‘yan sanda biyu tare da sace wasu shanu da ba a tantance adadinsu ba.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya fitar, ya ce bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sandan da ke sintiri ta garzaya zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka yi artabu da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta wa ‘yan fashin tserewa, cikin dajin da raunukan harbin bindiga kuma an yi nasarar kwato wasu shanun da aka sace.
Sanarwar ta ce, kwamishinan ‘yan sanda Bello Mohammed Sani, ya kai ziyarar tantancewar a wurin, inda ya ziyarci mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, inda ya jajanta masa tare da yi masa bayani kan kokarin, na hadin gwiwar hukumomin tsaro wajen yaki da miyagun laifuka a yankin.
Yayin da yake jaddada kudirin rundunar na yaki da kalubalen tsaro a jihar Kebbi,
CP Sani, ya yi Allah wadai da wannan mummunan lamari, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan jami’an ‘yan sandan da suka rasu ya kuma baiwa iyalansu da masu fatan alheri da juriyar wannan rashi mara misaltuwa.
PR/ Abdullahi Tukur/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
