Ilimi
Al’ummar Musulmi Sun Yi Addu’a Ta Musamman Ga Gwamna Kefas
Al’ummar musulmin jihar Taraba sun gudanar da karatun kur’ani mai tsarki tare da gudanar da addu’o’i na musamman ga gwamna Agbu Kefas da al’ummar jihar Taraba.
An gudanar da addu’ar ce a masallacin Juma’a na Saurara da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar Asabar 4 ga watan Janairu, 2025.
An fara shirin ne da karatun kur’ani mai tsarki, sannan aka gudanar da addu’o’i na musamman karkashin jagorancin manyan limamai na wasu masallatan Juma’a na jihar.
A karkashin jagorancin Malam Hussaini Isma’ila, mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin addinin musulmi, taron ya hada manyan limamai da malaman addinin musulunci daga kananan hukumomin jihar 16.
Malaman addinin Islama sun nuna godiyarsu ga Gwamna Agbu Kefas bisa namijin kokarin da yake yi na gina babbar jihar Taraba ga kowa da kowa.
A cikin addu’o’in da suka yi, malamai sun roki Allah ya ci gaba da yi masa jagora, ya ba shi lafiya, da nasara mai dorewa ga Gwamna da tawagarsa.
Malam Hussaini Ismaila, mai baiwa gwamna Agbu Kefas shawara kan harkokin addinin musulmi, ya karkare taron da kira ga ‘yan uwa musulmi na jihar Taraba da su hada kai da goyon bayan gwamnatin Gwamna Kefas.
Taron addu’o’i na musamman da Malam Hussaini Isma’ila ya shirya ya nuna kyakykyawar alaka tsakanin al’ummar Musulmi da gwamnatin Gwamna Agbu Kefas a halin yanzu, da kuma sadaukarwar da suke yi na samar da zaman lafiya da hadin kai da ci gaba.
Sani Sulaiman/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
