Connect with us

Labarai

An Gano Gawarwakin ‘Yan Cirani 27 Bayan Kifewar Jirgin Ruwa A Tekun Tunisia

Published

on

 

Jami’an da ke tsaron gabar tekun Tunisia sun tsamo gawarwakin ‘ƴan cirani 27 bayan nutsewar jirgin ruwan da suke ciki, a lokacin da suke ƙoƙarin ƙetara Tekun Meditareniya don tsallakawa Turai, sannan suka samu nasarar ceto mutane 87 da ransu.

A cewar babban jami’in da ke kula da gabar tekun, Zied Sdiri, sun gano gawarwakin ‘ƴan ciranin da lamarin ya rutsa da su ne a tsibirin Kerkennah, kuma sun fito ne daga yankin yammacin Sahara.

Sdiri ya ce an  garzaya da  mutane 15 daga cikin wadanda suka ceto zuwa asibiti, duk da dai bayyi ƙarin bayani kan hakan ba.

Wani jami’in rundunar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, ‘ƴan ciranin su 110 sun yi ƙoƙarin yin amfani da ƙananan jiragen ruwan don silalewa cikin daren Talata su tsallaka Turai.

‘Yan cirani daga Afrika dai na amfani da Tunisia da kuma makwabciyarta Libya don tsallakawa Turai, duk kuwa da hatsarin da hakan ke da shi.

 

RFI

Labarai

Labarai23 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara