Ilimi
An Bukaci Ma’aurata Su Rika Neman Sani Kafin Su Fara Tara ‘Ya’ya
An bukaci ‘yan Najeriya da su halarci zaman nasiha kafin rungumar aikin tarbiyyar yara domin samun nasarar samun iyali.
Wata kwararriyar kare hakkin yara kuma mai bada shawarwari akan harkokin rayuwa, Misis Gbemisola Osagede-Daramola ta yi wannan kiran yayin da take zantawa da manema labarai a Ilorin.
A cewarta akwai basirar tarbiyyar da ma’aurata ke bukata kafin su karbi aikin tarbiyyar yaran da zasu haifa
Ta bayyana cewa galibin ma’aurata da iyaye ba sa fahimtar aikin nasiha da horar da ’yan uwansu kafin su yi tsalle cikin harkokin auratayya.
Daramola ta jaddada bukatar kafa makarantar koyar da tarbiyyar yara domin koyar da matasa ma’aurata abubuwan da suka shafi tarbiyyar yara.
Ta shawarci ma’aurata da su rika zuwa neman shawarwari kafin aure kafin su shiga tarbiyyar yara, ta kara da cewa ba za a iya koyan irin wadannan abubuwan ta hanyar bincike na google ba.
Masaniyar kare hakkin yara ta bukaci iyaye da su samar da lokaci ga ’ya’yansu, maimakon ba da fifiko ga sana’o’insu.
Ta kuma yi kira ga iyaye su daidaita harkokinsu na yau da kullum da tarbiyyar ‘ya’yansu da tarbiyyar da ta dace.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
