Labarai
Zamu Tabbatar Da Anyi Bukukuwan Sallah Lafiya A Kebbi – ‘CP Chris

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, Chris Aimionowane, ya umurci, jami’an ‘yan sanda su ci gaba da aikin su na tabbatar da tsaro kafin da kuma lokaci da bayan bukukuwan Sallaha karama da za a fara gobe laraba..
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar yayin da yake taya al’ummar musulmin jihar murnar kammala azumin watan Ramadan na bana yana yi wa daukacin al’ummar musulmi barka da Sallah.
Sanarwar ta yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwan domin yin tunani da kuma yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki daya.
Haka kuma ta yi kira ga malaman addini da masu ibada da mazauna jihar da su ba ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin kai a jihar domin an samar da isasshen tsaro domin tabbatar da gudanar da bukukuwan sallah a jihar cikin kwanciyar hankali.
Yayin da yake gargadin duk masu tayar da hankali da mugun nufi da wani yunkurin kawo cikas ga bikin da su kaurace wa jihar, ya kuma umarci mutanen jihar Kebbi na gari da su ci gaba da zaman lafiya tare da gudanar da bukukuwa cikin kwanciyar hankali da lumana.
PR/Abdullahi Tukur/Wababe
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
