Labarai
Za A Samarda Tsaro Lokacin Bukin Sallah A Nasarawa – Kwamishina

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce an samar da isassun matakan tsaro domin tabbatar da gudanar da bukukuwan Sallah ba tare da tangarda ba a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Umar Shehu Nadada ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a garin Lafia babban birnin jihar.
Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sandan a lokacin da yake taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan na bana tare da yi wa dukkan musulmi fatan bukukuwan Sallah lafiya. Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su yi amfani da lokacin bukukuwan domin yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki daya.
Kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga malaman addini, masallata da mazauna jihar da su ba ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro hadin kai, domin ya tabbatar da cewa an yi kokarin inganta tsaro a lokacin bikin sallah karama.
Sanarwar ta kuma umurci dukkan kwamandojin ‘yansanda na yankin da shugabannin sassan da kuma jami’an ‘yan sanda na sassan jihar da su rika sanya ido domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da samar da tsaro a duk wuraren ibada da na shakatawa da kuma kai samame a wuraren da aka gano akwai matsala.
Don haka kwamishinan ‘yan sandan ya umarci al’ummar jihar da su kasance masu zaman lafiya da gudanar da bukukuwa cikin kwanciyar hankali.
Idan kuma wata matsala ta taso, ana kira ga jama’a kada suyi kasa a gwiwa wajen kiran wadannan lambobin waya kamar haka: 08036157659, 08032564469, 08112692680 da 08104441179.
Rel/Aliyu Muraki/Lafia/Wababe
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
