Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Karrama Bill Gates Da Lambar Girmamawa Ta CFR

Published

on

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin  masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman.

Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa.

Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata.

Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate, ya ce karramawar da aka yi wa Mista Gates ta cancanta kwarai,  idan aka yi la’akari da irin gagarumar rawar da ya taka a ci gaban Najeriya.

Farfesa Pate ya bayyana cewa taimakon da Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta bayar ya taimaka sosai wajen kawar da cutar shan inna (polio) a kasar.

Yayin da yake gode wa Shugaban Kasa bisa karramawar CFR, Mista Gates ya ce yaki da cutar shan inna daya ce daga cikin mafi wahala da Gidauniyarsu ta yi, sai dai hakan ya sa su hada kai da sarakunan gargajiya don cimma nasara.

Ya bayyana cewa Gidauniyar ta kaddamar da allurar rigakafin cutar HPB don rage mace-macen mata kimanin 7,000 a shekara sakamakon cutar sankarar mahaifa.

Mista Gates ya bayyana cewa allura guda daya kacal da ake bai wa ‘yan mata masu shekaru 9 zuwa 14 na iya basu kariya na daga cutar.

Gates ya tabbatar wa Shugaban Kasa cewa zai ci gaba da jajircewa wajen inganta lafiya a Najeriya, inda ya ce yana da niyyar amfani da dukiyarsa gaba daya wajen wannan aiki cikin shekaru ashirin masu zuwa.

Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Dangote, Ministan Harkokin Musamman da Hulda tsakanin Gwamnati, Zephaniah Jisalo, manyan jami’an Gidauniyar Gates, da Dakta Ayuba Burki Gufwan, Sakataren Gwamnati na Hukumar Kula da Masu Bukata ta Musamman na Kasa, na daga cikin wadanda  suka halarci bikin karramawar.

Daga Bello Wakili

Labarai

Labarai8 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara