Ilimi
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Kafa Dokar Wuraren Tsaro A Makarantu
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fara aiki kan dokar da za ta kafa wuraren tsaro (safe spaces) a makarantu domin karfafa ilimin yara mata a jihar.
Shugaban Kwamitin Ilimi, Honarabul Mahmud Lawal, ya bayyana hakan a babban taro kan Ilimin Yara Mata da aka gudanar a Zariya, wanda Cibiyar Kula da Ilimin Yara Mata (CGE) ta shirya don tunawa da Ranar Yara Mata ta Duniya ta 2025.

Ya ce dokar, mai taken “Dokar Wuraren Tsaro a Jihar Kaduna, 2025,” za ta kare ‘yan mata daga cin zarafi, hana wariya, da samar da tsarin horaswa da rahoto a makarantu.
Daraktar CGE, Hajiya Habiba Mohammed, ta ce taron na da nufin kara karfafa ‘yan mata a matsayin shugabannin da za su kawo sauyi, musamman a lokacin rikice-rikice da suke fuskantar kalubale irin su aure da wuri da barin makaranta.

Ta ce cibiyarsu na ganin ilimi a matsayin makamin da zai bai wa ‘yan mata damar canza al’umma, kuma dokar majalisar za ta taimaka wajen tabbatar da shirye-shiryen su a makarantu.
A jawabinsa a wurin taron, Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Farfesa Adamu Ahmed, ya yaba da taken taron, yana mai cewa ya dace da kalubalen da ‘yan mata ke fuskanta.

Ya ce daya cikin kowanne ‘yan mata hudu a yankin na yin aure kafin shekaru 18, kuma har yanzu ba su da daidaiton damar ilimi kamar maza.
Farfesa Ahmed ya bayyana cewa ABU na kara yawan ‘yan mata da take karɓa, inda suka kai kashi 42 cikin 100, tare da kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su kara zuba jari a ilimin ‘yan mata.
Ibrahim Suleiman
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
