Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Horas Da Yara Sana’o’i Tun Daga Matakin Firamare

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ta hanyar samar da tsari na ƙasa kan haɓaka sana’o’in hannu daban daban.

An bayyana hakan ne a taron Cibiyar Horas da Sana’o’i ta Kasa da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da Ministan Ilimi a matsayin mataimakinsa.

Bayan kammala taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa tattaunawar ta haifar da Ɗa mai ido, inda ya ce za a aika da kudirin kafa Cibiyar Horas da Sana’o’i ta Ƙasa  zuwa majalisar dokoki nan ba da daɗewa ba.

Ya ce: “Manufar ita ce a daidaita ayyukan dukkan manyan masu ruwa da tsaki a wannan fanni. Kaduna ta riga ta amfana ƙwarai, inda Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da cibiyoyin koyon sana’o’i, inda  dalibai sama 32,000 ke koyon sana’o’i daban daban.

Ministan Ilimi, Farfesa Tunji Alausa, ya jaddada cewa horar da sana’o’in hannu na kan gaba a cikin ajandar  gwamnati, wacce ke daidai da alƙawarin Shugaba Tinubu na samar da damar ci gaba ga matasan Najeriya.

Ya bayyana cewa sabuwar manhajar ƙasa yanzu ta mai da hankali ne sosai kan fannoni na musamman guda shida, da suka hada da ɗinki, kiwon dabbobi, gyaran kwamfuta da wayoyin hannu, da sauransu, waɗanda su ne sana’o’in da kasa ke matukar bukata a yanzu.

Ita kuwa Minista a Ma’aikar  Kwadago da Samar da Ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha, ta bayyana cewa Majalisar  Zartaswa na kokarin tabbatar da cewa yara na samun horo kan sana’o’in hannu tun daga matakin farko na ilimi har zuwa girmansu.

Ta ce “Manufar ita ce a tabbatar kowanne yaro ya girma da wata kwarewa, don rage tarin matasan da ba su da aiki. Haku kuma kowa zai samu damar taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma.”

 

Bello Wakili

Labarai

Labarai3 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai23 hours ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai1 day ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai1 day ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai1 day ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara