Labarai
Gwamna Bago Ya Bayyana Gamsuwarsa Game Da Aikin Gyaran Asibitin IBB
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana gamsuwarsa da aikin sake fasalin Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ya duba aikin fadada asibitin da ake yi, inda ya yaba wa ‘yan kwangilar da ke gudanar da aikin bisa inganci.
Umar Bago ya yi amfani da wannan dama wajen jaddada kudirin gwamnatinsa na farfado da bangaren kiwon lafiya, domin bai wa al’ummar jihar Neja damar samun ingantacciyar kulawa.
Tun da farko, gwamnan ya ayyana dokar ta baci a fannin lafiya, inda aka fara tsauraran gyare-gyare, sake ginawa da kuma sabunta cibiyoyin kiwon lafiya a sassan jihar.
Ana cigaba da gyare-gyare a Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna, inda aka kammala sabunta bangarori kamar na gaggawa (Emergency/Accident Unit), Sashen Majinyata na Gabaɗaya (General Outpatients Department), Sashen Kulawa na Musamman (ICU), ofisoshin likitoci da Nas Nas, da kuma sashen gadajen majinyata na musamman (VIP Units), tare da samar da kayayyakin zamani na lafiya.
Bayan haka, an gina gidajen likitoci guda biyu masu dakuna biyu kowanne, da kuma tankin ruwa mai daukar lita 42,000 a sama, da ƙara gina rijiyar burtsatse.
Haka kuma, an samar da na’urar Elizer da ke duba jinin ɗan adam, tare da sabon janareta mai ƙarfin KV 100 domin cibiyar gwaje-gwaje ta NNPC, da kuma janareta mai ƙarfin 300 KVA, tare da wasu na’urori da ake amfani da su a asibitin.
Daga Aliyu Lawal
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
