Labarai
Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Shirin Inganta Rayuwar Matasan Da Suka Tuba Daga Ayyukan Daba
Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar Hukumar ’Yan Sanda ta Ƙasa sun kammala binciken matasa 718 da suka daina harkar daba a ƙarƙashin shirin ‘Safe Corridor Project’ na jihar.
Wannan mataki muhimmin tsari ne na rage rashin tsaro da kuma bai wa matasa masu rauni damar zama nagari.
Bikin ƙaddamar da shirin ya gudana ne a ginin ‘yan sanda na officers’ mess da ke Bompai a Kano. A wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana shirin afuwar a matsayin dabarar zaman lafiya wajen magance laifuka da tashin hankali a jihar.
Gwamnan wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Alhaji Ibrahim Waiya ya wakilta, ya bayyana cewa ƙarin matasa 960 da suka tuba na jiran tantancewa a mataki na gaba. Yana mai cewa an tsara shirin ne don kawo ƙarshen matsalolin tada-zaune-tsaye, satar waya da sauran laifuka, ta hanyar bai wa masu tuba damar gyara rayuwarsu don sake dawowa cikin al’umma, da kuma samun taimakon dogaro da kai.
“Mun yi imanin cewa idan muka rungumi waɗannan matasa ta hanyar wannan dabarar zaman lafiya, za mu iya shawo kan ƙalubalen da muke fuskanta na fadan daba, wanda ya daɗe yana damun al’umma. Babban burinmu shi ne mu sa harkar daba ta zama tarihi a Kano.” In ji Gwamna Yusuf.
Ya ƙara da cewa za a yi wa matasan gwajin miyagun ƙwayoyi karkashin shirin gyaran dabi’u na hukumar yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA. “Waɗanda suka tsallake wannan mataki za su samu tallafi daga gwamnati domin dogaro da kansu, don kauce wa komawa ga aikata laifi”. In ji shi.
A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba da ƙoƙarin gwamnati tare da tabbatar da aniyar hukumar ’yan sanda na ci gaba da tallafa wa shirin.
Ya jaddada cewa yaƙi da laifuka ba na ’yan sanda ba ne kaɗai, ya bukaci iyalai da al’umma su rungumi wannan aiki tare da hukumomin tsaro.
Shi ma Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris, ya bayyana goyon bayan hukumar ga shirin ‘Safe Corridor Project‘. Yana mai cewa amfani da miyagun ƙwayoyi na daya daga cikin abubuwan da ke jefa matasa cikin tashin hankali, ya kuma jaddada muhimmancin ganin gwamnatin ta kara zage dantse domin samun zaman lafiya a jihar.
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun shawarci matasan da su tsaya tsayin daka a kan tubansu, suna gargadin cewa kada su yi asarar wannan dama da gwamnati ta basu.
Su ma wasu daga cikin matasan da suka tuba da suka yi jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, sun gode wa gwamnati bisa wannan tsari, tare da yin alƙawarin zama ’yan ƙasa masu zaman lafiya da amfani a cikin al’umma.
Abdullahi Jalaluddeen
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
