Labarai
Jihar Kwara Ta Bukaci Gwamnatocin Jihohi Su Tallafawa Kokarin Hukumar NOA Don Inganta Rayuwar Al’umma
Gwamnatin Jihar Kwara ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da tallafawa Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) domin tabbatar da cimma manufarta ta gyara dabi’u da wayar da kan jama’a a fadin jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Jibril Saba ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi tawagar hukumar a ofishinsa da ke Ilori.
Ya jaddada cewa rawar da NOA ke takawa a fannonin da suka hada da koyar da ɗabi’un nagari, wayar da kan al’umma, da cewa abin a yaba ne matuka.
Farfesa Saba ya bayyana cewa ya zama wajibi ga gwamnatocin jihohi su ba da hadin kai da tallafi ga hukumar domin ta iya samar da tasirin da ake bukata a cikin al’umma.
A cewarsa, “muna cikin wani zamani da abubuwa da dama ke tafiya ba daidai ba a cikin al’umma, daga miyagun laifuka zuwa shan miyagun ƙwayoyi, ta’addanci da sauran dabi’un da ba su dace ba – musamman a tsakanin matasa.”
Farfesa Saba ya tabbatar wa hukumar da jajircewar gwamnatin jihar wajen mara mata baya a dukkan ayyukanta.
A nasa jawabin, Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) reshen Jihar Kwara, Alhaji Abdulganiyu Dare, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa ci gaba da ayyukan raya ƙasa a fannoni daban-daban.
Ya kuma roƙi ƙarin tallafi daga gwamnatin jihar domin ba hukumar damar fuskantar ƙalubalen al’umma da ake buƙatar shawo kansu kusan kullum.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha4 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai4 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai3 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai3 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai3 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai3 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
-
Labarai3 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
