Labarai
Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Raba Kayayyakin Lafiyar Mata Da Yara Kyauta
Hukumar Kula da Lafiya A Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta fara raba kayayyakin kula da mata masu juna biyu, da kananan yara kyauta a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 106 a fadin jihar.
Wannan shiri na daga cikin alkawuran Gwamna Abba Kabir Yusuf na inganta damar samun lafiya ga mata da yara.
A yayin bikin kaddamar da rabon, Darakta Janar na KSPHCMB, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya bayyana cewa kayayyakin za su taimaka wajen rage mace-mace da ake iya kaucewa na mata masu juna biyu da yara, ta hanyar karfafa tsarin lafiyar matakin farko a Kano.

Ya umurci Daraktocin Yankuna da Shugabannin Sassa (HODs) da su tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen rabon kayayyakin.
Darakta Janar din ya gargadi duk wata karkatarwa ko almundahanar kayayyakin, inda ya jaddada cewa hukumar za ta sa ido sosai don tabbatar da cewa kayan sun isa ga wadanda suka dace.
Farfesa Salisu ya jinjinawa Gwamna Abba bisa cika alkawuran zabe da kuma fifita lafiyar mata da yara, tare da godewa Kwamishinan Lafiya, Dr. Labaran Abubakar Yusuf, bisa goyon baya da kyakkyawan jagoranci wajen ci gaban harkar lafiya a jihar.

Shi ma Daraktan Sashen Magunguna, Pharmacist Abdullahi Abubakar Danzabuwa, ya tabbatar da cewa kayayyakin suna da inganci sosai, kuma za a raba su bisa ka’idojin kasa da kasa na tsarin rabon magunguna da kayayyakin lafiya.
Hukumar ta KSPHCMB ta bayyana tabbacin cewa shirin zai inganta lafiyar mata da yara a jihar Kano, tare da kara tabbatar da jihar Kano a matsayin jagora a harkar lafiya a matakin farko a Najeriya.
Daga Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
