Labarai
An Kaddamar Da Dashen Itatuwa A Rukunin Gidaje Na Danmodi Da Ke Birnin Kudu
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba ya kaddamar da dashen itatuwa a rukunin sabbin gidaje na Danmodi dake a Jihar Jigawa.
A jawabin sa, Dr Builder Uba ya bukaci jama’ar yankin da su rungumi dashen itatuwa domin samun lada da kuma yaki da kwararowar hamada.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban sashen aikin gona, Malam Muktar Idris Gumel ya shawarci kungiyoyi da su rika sa ido wajen kula da dashen itatuwa.
Wakilinmu ya shaida mana cewar, an dasa kimanin bishiyoyi 300, yayin da za’a ci gaba da yin dashen a sauran wurare da ake bukatar hakan a fadin Karamar Hukumar ta Birnin Kudu.
Dashen itatuwan na daga cikin kudurorin shugaban karamar hukumar na magance matsalar hamada da zaizayar kasa da kuma sauyin yanayi
Kazalika, anyi tanadin dashen itatuwa dubu 100 domin dasawa a bana kamar yadda Gwamna Umar Namadi ya tanadar.
Bikin ya samu halartar kungiyoyin matasa da dama.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
