Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Dauki Nauyin Aurar Da Mata 300 Kafin Azumi

Published

on

Gwamnatin jihar Kebbi, ta kammala shirye-shiryen gudanar da daurin auren mata dari uku a karshen watan Fabrairun wannan shekara.

Da yake zantawa da manema labarai da yammacin Lahadi, shugaban babban kwamitin kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Suleiman Muhammad Argungu, ya bayyana cewa, nasarar daurin auren da aka yi a shekarar da ta gabata, wanda gidauniyar NANAS ta uwargidan Gwamnan, Hajiya Nafisa ta shirya, ya sanya gwamnatin ta sami kwarin gwiwar daukar nauyin aurar da wasu rukunin a wannan shekarar.

A cewar Shugaban kwamitin, za a aurar da mutane  600  marasa galihu ba tare da la’akari da addini, kabilanci da siyasa ba a tsarin gwamnati.

Ya ce, an kafa kwamitocin tantancewa a dukkan kananan hukumomi 21 domin zabar ma’auratan da suka cancanta bisa ka’idojin da aka gindaya wadanda suka hada da tabbacin  ango yana da abin yi do daukar nauyin iyalansa, da kuma matsugunin da za su zauna.

Suleman Argungu, ya bayyana cewa, dukkan ma’auratan za a yi musu gwajin lafiya na tilas, ciki har da gwajin kwayar cutamai karya garkuwar jiki ta  HIV, da kwayoyin halitta na Genotype.

Za a biya  Naira 180,000 a matsayin sadaki ga kowace amarya, wanda ya kama jimillar Naira miliyan 54, tare da kayan daki, da suka katifa, gado da kuma kayan amfanin gida.

Daga Abdullahi Tukur

Labarai

Labarai8 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara