Labarai
Fasinjoji 85 Sun Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Hatsarin Jirgin Sama A Senegal
Wani jirgin sama samfurin 737 dauke da mutane 85 ya tsallake rijiya da baya a filin jiragen sama na Dakar, da ke kasar Senegal, inda ya raunata mutane 10, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Mawakin kasar mai suna, Mali Cheick Siriman Sissoko wanda ya wallafa yadda lamarin ya auku a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa, “Jirgin da muke ciki kawai ya kama da wuta,” yana mai cewa kururuwar mutane ta cika cikin jirgin a lokacin da al’amarin ya faru.
Ministan Sufuri El Malick Ndiaye ya ce jirgin Air Senegal ya nufi Bamako babban birnin kasar Mali da ke makwabtaka da kasar da yammacin Laraba, dauke da fasinjoji 79 sai kuma matukan jirgi biyu da ma’aikatansa guda hudu.
Wadanda suka jikkata dai suna karbar kulawar likitoci a asibiti yanzu haka, yayin da sauran kuma aka kai su otel domin su huta.
Har yanzu dai babu wani cikakken bayani kan musababbin faruwar hatsarin jirgin.
Cibiyar Safety Network mai bin diddigin hadurran jiragen sama, ta wallafa hotunan yadda jirgin ya kafe a cikin wani fili mai dauke da ciyawa a shafinta na X.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
