Labarai
Za a Dauki Mataki Kan Masu Cin Zarafin Yan Aikin Gida
A wani mataki na kare hakkin ‘yan aikin gida da ma kare iyayen gidan da ake yi wa aikin daga fuskantar wata matsala daga kowanne bangare, majalisar dattawan Najeriya ta ce akwai bukatar samar da hukumar da zata rika tattara bayanan ‘yan aikin da kuma iyayen gidan na su.
Majalisar ta ce za a samar da hukumar ne domin tabbatar da kare ‘yan aiki wadanda a ko da yaushe suke fuskantar cin zarafi daga wajen iyayen gidansu.
Sannan kuma a kare iyayen gidan da a wasu lokutan ke fuskantar hadari daga masu yi musu aikin.
Matakin samar da hukumar da majalisar ke shirin yi ya biyo bayan wani kuduri da daya daga cikin ‘yan majalisar sanata Babangida Hussaini, ya gabatar a zauren majalisar wanda kuma ya samu cikakken goyon baya da kuma tsallake karatu na biyu a majalisar.
Sanata Babangida Hussaini, ya ce rashin dokar da zata rinka sanya ido da kuma bibiyar irin wadannan al’amura da ma sanya ido a kansu ya sa cin zarafi ‘yan aiki ya yawaita a Najeriya.
Sanatan ya ce irin hakan kuma kan janyo faruwar manyan laifuka kamar kisan kai a tsakanin ‘yan aiki da iyayen gidansu.
Babangida Hussaini ya ce,” A wasu lokuta zaka ga ba a biyan ‘yan aiki hakkinsu kamar yadda ya kamata, wadansu ana cin mutuncinsu inda wadansu ma har rasa rayukansu suke.”
Ya ce,” A bangaren masu daukar ‘yan aikin gidan kuma wato iyayen gida ke nan ana samun matsaloli kamar hada kai da masu aikin gida da wasu bata gari wajen sace sace ko kuma wani lokacinma a lalata yaran gida.”
” Wannan duk ya biyo bayan rashin tsari da ma sanya idanu ne.” in ji shi.
Kudurin dokar samar da hukumar dai zai gindaya wasu sharuda da sai an cika su kafin a dauki ‘yar aiki ko dan aiki, sannan dole shi ma mai daukar ‘yan aikin a samu bayanansa.
Sanata Babangida Hussaini, ya ce idan wannan kudurin ya zama doka to akwai dokar da za ayi wadda iyayen gida ba za su rinka cin mutuncin ‘yan aiki ba, sannan wajibi ne kuma a rinka kula da ci da sha da wajen kwanan ‘yan aiki.
Bashir M
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
