Labarai
Muna Mika Sakon Ta’aziyar Mu Ga Al’ummar Iran – Tinibu
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa rasuwar shugaba Ebrahim Raisi; Ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, da wasu jami’ai a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana bakin cikinsa game da wannan bala’in, ya kuma bayyana shugaba Raisi a matsayin shugaba mai kishin ci gaban kasar Iran.
Yayin da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasu, shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya karawa al’ummar Iran zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba.
A madadin gwamnati da al’ummar Najeriya, shugaban ya tabbatar wa Jamhuriyar Musulunci ta Najeriya goyon baya da addu’a a wannan lokaci na bakin ciki.
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
