Labarai
Majalisar Dokokin Kano Ta Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Wadanda Harin Masallaci Ya Shafa
Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta taimaka wa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a harin masallaci da ya faru a karamar hukumar Gada Gezawa.
Wannan dai ya biyo bayan zaman tattaunawa ne da aka yi a zauren majalisar wanda shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jagoranta.
A wani kudiri na gaggawa wanda dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa Alhaji Abdullahi Yahaya ya gabatar ga majalisar, ya bayyana cewa mutane 17 ne suka rasu, yayin da wadanda ke raye ke cikin mawuyacin hali, wanda a halin yanzu suke samun kulawa a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Dan majalisar ya bayyana cewa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata na bukatar tallafi daga gwamnatin tarayya da na jihohi.
Abdullahi ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya bukaci hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gurfanar da wanda ya aikata laifin.
Sauran wadanda suka goyi bayan kudirin sun hada da wakilan Kiru da Madobi Usman da Sulaiman Mukhtar.
Tun da farko kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jajantawa gwamnati da iyalai da daukacin al’ummar jihar bisa wannan mummunan lamari da ya faru, inda ya yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka rasu ya kuma ba sauran lafiya.
A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi gyaran fuska ga kudirin gudanar da kasafin kudi a karatu na biyu.
Shugaban masu rinjaye wanda dan kuma shi ne dan majalisa mai wakiltar, Dala Alhaji Lawan Hussaini Dala ya yi nuni da cewa dokar tana neman tabbatar da ‘yancin cin gashin kai ga majalisar dokokin Kano kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus-alawus, daukar ma’aikata, karin girma da sauransu.
Da yake goyan bayan kudurin, mataimakin shugaban majalisar Alhaji Muhammad Bello Butu Butu ya jaddada cewa, bayan an yi nazari an lura akwai banbance-banbance tsakanin kudurin kula da kudade na majalisar dokokin Kano da na majalisar kasar, don haka akwai bukatar gyara.
Majalisar ta dage zamanta zuwa washegari a wani kudiri da shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini Dala ya gabatar.
Khadija Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
