Connect with us

Labarai

Sojin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo Sun Daƙile Yunkurin Juyin Mulki

Published

on

Jamhuriyar Dimokaraɗiyar Congo ta ce ta daƙile wani yuƙurin   kifar da gwamnatin shugaba Felix Tshisekedi a  Kinshasha, kuma har da ƴan  ƙasashen waje a cikin masu  wannan yunƙuri.

Lamarin ya auku ne da safiyar Lahadi a kusa da gidan ministan tattalin arzikin ƙasar, Vital Kamerhe, a yankin Gombe da ke arewacin babban birnin ƙasar, kamar yadda rahotanni  suka bayyana.

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar ƙasar, kakakin rundunar sojin ƙasar, Janar Sylvain Ekenge ya tabbatar da lamarin, inda ya ce an kashe jagoran masu yukurin juyin mulkin, tare da kama mutane 50 da ke da hannu a ciki da suka haɗa  da wasu Amurkawa da dama da wani ɗan Birtaniya guda.

Janar Ekenge ya ce ɗan ƙasar Congon da ya jagoranci yunƙurin kifar da gwamnatin shi ne, Christian Malanga, wanda ya ke da takardar zama ɗan Amurka, kuma tuni dakarun Congo suka harbe shi.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa an ji ƙararrakin harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasar a lokacin yunƙurin juyin mulkin.

Jakadan Amurka a Kinshasha ya bayyana kaɗuwarsa a kan lamarin da ya auku, a yayin da Tarayyar Afrika ta caccaki yunƙurin na kifar da gwamnatin farar hula.

Masu yunƙurin juyin mulkin sun shirya kai farmaki gidan sabuwar fira ministar ƙasar, Judith Suminwa, da kuma na mministan tsaro, Jean-Pierre Bemba, amma kuma sai suka gaza gane gidan Suminwa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara