Labarai
Kwamitin Yiwa Hisba Granbawul Ya Mika Rahotonsa A Jigawa

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi rahoton kwamitin Hisba da aka kafa domin duba tsari da ayyukan Hisba a jihar.
Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin bitar, wanda kuma shine sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Ibrahim, ya ce akwai nakasu a cikin dokokina ake da su, wanda hakan ya janyo gurgunta ayyukan Hisba.
Ya ce babban aikin kwamitin nasu ya mayar da hankali ne kan sake duba tsarin shari’a domin kiyayewa ko duba dokokin da ake da su.
Ya ce muhimman shawarwarin rahoton sun hada da kara yawan ma’aikata tare da samar da isassun kudade domin karfafa aikin hukumar.
Alhaji Bala Ibrahim ya bayyana cewa, a halin yanzu ma’aikatan Hisba 1,700 a fadin jihar ba su isa su iya gudanar da ayyukan hukumar ba.
Don haka rahoton ya ba da shawarar cewa adadin ma’aikatan ya kai 4,600.
A nasa jawabin gwamna Umar Namadi ya ce wannan na daya daga cikin muhimman kwamitoci da gwamnati ta kafa a jihar.
Ya kara da cewa rahoton yana da yalwa kuma idan aka aiwatar da shi, jihar za ta samu mafi kyawun hukumar Hisba a fadin kasar nan.
Gwamnan ya yabawa ‘yan kwamitin bisa jajircewa da kwazon da suka nuna, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta aiwatar da shawarwarin baki daya.
Namadi ya ce manufar ita ce a samu Hukumar Hisba mai inganci da aiki.
KARSHE/USMAN MZ/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
