Labarai
Ana Gasar Sarauniyar Kyau Ta Tumaki A Senegal
Tumaki a Senegal na gwagwarmayar lashe babbar kyautar gasar kyau da suke yi.
Tunkiyar da aka fi sanya ran zata lashe gasar itace Guediawaye wadda ta fito daga wani ƙaramin ƙauye gab da birnin Dakar.
Bayanai sun ce Tunkiyar Jinsin Niang Ballo, waɗanda basu da yawa a ƙasar, inda ake sanya su a cikin Tumaki mafiya kyau da ɗaukar ido la’akari da yanayin girman hallita da kuma sassan jikinsu.
Mamallakin Tunkiyar Muhammed Wane, ya ce baya jin ko ɗar cewa Tunkiyarsa ce zata yi nasara, yana mai cewa ko bayan kyan tsarin hallita da Allah yayi mata, tafi kowacce Tunkiya ɗaukar kwalliya a cikin jerin Tumakin da suka shiga gasar.
Tun fara gasar Tumkiyar ta lashe kyaututtuka fuda takwas, tun tana ‘yar karamarta zuwa yanzu.
Masu shirya gasar sun ce an rabbare ɓangaren kyau na Raguna da Tumaki daban, sai kuma matasa, kuma an shirya ta ne don ƙarfafawa makiyaya gwiwar kulawa da dabbobinsu.
A cewar makiyayan irin waɗannan nau’ikan Tumaki, ba ana kiwon su ne don ci ba, a’a ana kiwata su ne don ado da ƙawata gida.
Bayanai sun nuna cewa mafi yawan mutanen da ke kiwon irin waɗannan Tumaki masu arziki ke, la’akari da irin tsadar da take da shi.
Muhammad Wane ya shaidawa manema labarai cewa an taya masa Tunkiyar tasa ta Niang Ballo kan kuɗi dala dubu 100, amma ya ki sayarwa.
Tuni dai aka fara sanar da sakamakon Gasar, inda ɗan rago Alou, mallakin Maniane Ndaw yayi nasara a ɓangaren matasan Raguna.
rfi
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
