Labarai
Gwamnan Jihar Kwara Ya Raba kudi Da Filaye Ga ‘Yan Wasan Jihar
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Kwara United bayan da suka zama zakaran gasar cin kofin shugaban kasa na 2025.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran Rafiu Ajakaye ya fitar ya ce gwamna AbdulRazaq ya kuma karbi bakuncin rukunin ‘yan kasa da shekara 19 na kungiyar da ta lashe gasar matasa ta kasa karo na farko.
Ta ce gwamnan ya bai wa kowanne dan wasan Kwara United kyautar naira miliyan biyar da fili a babbar karamar hukumar ta Kwara Smart City, inda ya yaba musu bisa yadda jihar ke alfahari.
Ta ce kungiyar ta Kwara United ta doke takwarorinta na Abakaliki FC a wasan da aka kamala da bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan wasan na mintuna 90.
Tawagar ta yi nasarar shiga Ilorin ne a ranar Litinin da yamma, inda mazauna babban birnin jihar suka yi ta daga hannu da jinjina ga dogayen ayarin motocinsu daga Eiyenkorin zuwa dakin liyafar da ke gangarowar GRA inda aka gudanar da liyafar.
liyafar ta samu halartar manyan baki da dama ciki har da shugabar kwamitin majalisar dokokin jihar Kwara kan harkokin wasanni Hon Rukayat Shittu.END
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
