Labarai
An Kashe Makiyaya 2 Da Shanu 150 A Sabon Hari A Filato

Aƙalla makiyaya biyu da shanu 150 ne rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun kashe a wani hari da suka kai gundumar Kwal da ke Ƙaramar hukumar Bassa a Jihar Filato.
A cewar shugabannin Fulani a jihar, an kuma yi awon gaba da shanu sama da 100 a lokacin da lamarin ya faru.
Shuwagabannin Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da na takwararta Gan Allah Fulani (GAFDAN), Nura Abdullahi da Garba Abdullahi, sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.
Sun bayyana cewa akwai yiwuwar adadin shanun da aka kashe sun kai fiye da 150, yayin da wasu da dama suka ɓace.
Da yake bayyana lamarin, shugaban GAFDAN ya ce, “Makiyayan suna kiwon shanunsu ne da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Laraba, kwatsam wasu ‘yan bindiga suka buɗe musu wuta.
“Sun harbe makiyaya biyu har lahira. Har ila yau, sun harbe ɗaruruwan shanu, inda suka kashe kimanin 150.
“Har yanzu ba mu tabbatar da yawan ɓarnar ba, domin lamarin ya faru ne a wani wuri mai nisa da ke da wahalar shiga, ba tare da jami’an tsaro ba. Mun yi babban rashi.
“Lokaci ya yi da jami’an tsaro za su ɗauki mataki kan ta’asar da ake yi wa mutanenmu.
“A duk lokacin da aka kai mana hari, sai jami’an tsaro su nemi mu kwantar da hankalinmu.
“Wannan yunƙuri ne na halaka mu, kasancewar hari ne na ba gaira ba dalili. Muna kira ga hukumomin tsaro da su kawo mana agaji.”
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta ‘Operation Safe Haven’ a jihar, Manjo Samson Zhakom, sai dai haƙar ba ta cimma ruwa ba har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
-
Labarai4 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai5 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai1 day agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai5 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai2 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai5 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai4 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
