Labarai
An Nada Kabir Yahaya Darakta Janar na Farko na Filin Jirgin Sama da ke Gusau
Daga Aminu Dalhatu
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Kabir Yahaya Gusau a matsayin Darakta Janar na farko na Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa da ke Gusau.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana hakan a Gusau, inda ya ce naɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin wajen tabbatar da ingantaccen tsari da kuma shirya filin jirgin domin fara aiki nan ba da jimawa ba.
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Sakataren Gwamnatin Jihar, Sulaiman Ahmad Tudu ya fitar, ana sa ran filin jirgin zai ƙara bunƙasa haɗin kai na zirga-zirgar jiragen sama zuwa ƙasashen waje, da jawo damar zuba jari, tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arziƙi a Jihar Zamfara da ma Najeriya baki ɗaya.
Sanarwar ta ce Kabir Yahaya Gusau ƙwararren masani ne a fannin harkokin sufurin jiragen sama, wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana aiki a fannoni daban-daban na gudanar da ayyukan jiragen sama da sarrafa sararin samaniya.
Ya riƙe muƙamai masu muhimmanci a fannin sufurin jiragen sama a Najeriya, ciki har da Manajan Sararin Samaniya a Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Kasa a Filin Jirgin Sama na Gombe, da kuma Mataimaki na Musamman ga Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar.
Kafin wannan naɗi, shi ne Babban Manaja na Sashen Bayanan Sufurin Jiragen Sama (Aeronautical Information Services) a hedikwatar Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Kasa da ke Abuja.
Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci sabon Daraktan Janar ɗin da ya yi amfani da gogewarsa wajen tabbatar da ingantaccen tsari da gudanar da ayyukan filin jirgin yadda ya kamata, bisa ƙa’idojin sufurin jiragen sama na duniya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
