Labarai
Ramadan: Sarkin Kauru Ya Bukaci a Kara Karfafa Tsoro Tare da Tallafawa Marasa Galihu
Daga Yusuf Zubairu Kauru
Sarkin Kauru da ke Jihar Kaduna, Alhaji Zakari Ya’u Shehu Usman, ya yi kira da a kara inganta tsaro a yankin, inda ya bukaci hukumomi su rika sa ido sosai kan masu ba da bayanan sirri, tare da samar wa jami’an tsaro isasshen tallafi domin su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin taron bude baki na watan Ramadan na shekara-shekara da ake gudanarwa a ranar 15 ga watan Ramadan a fadarsa da ke Kauru.
Sarkin ya kuma bukaci al’umma su kara dagewa da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan, yana mai cewa manoma na fuskantar kalubale masu yawa sakamakon tashin farashin kayayyakin abinci, lamarin da ke shafar rayuwarsu da harkokin noma.
Ya kuma jaddada muhimmancin karfafa dankon zumunci musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan, tare da karfafa gwiwar jama’a da kungiyoyi su rika taimakawa marasa galihu ta hanyar bayar da abinci da sauran tallafi.

Makaman Kauru, Alh Umaru Abubakar

Hakazalika, Sarkin ya yabawa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, kan ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ke aiwatarwa wadanda ke kawo sauyi mai ma’ana ga al’ummomin Karamar Hukumar Kauru.
Daga karshe, ya bukaci mazauna yankin su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai, tare da dagewa da yin addu’o’i domin samun dawwamammen zaman lafiya a fadin kasar nan.

Rediyon Najeriya Kaduna ta rawaito cewa Sarkin ya rufe taron da addu’o’in samun zaman lafiya da cigaba, tare da rokon Allah ya kara wa masarautar daukaka.
-
Labarai4 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai2 days agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai6 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai5 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai5 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai5 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
