Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta Amince da Kudirin Kasafin 2026

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da Kudirin Dokar Kasafin Kuɗin shekarar 2026 na sama da naira biliyan 901, tare da sanya hannu ya zama doka, bayan yin wasu gyare-gyare.

Wannan ya biyo bayan gabatarwa da kuma amincewa da rahoton Kwamitin Majalisar kan Kasafin Kuɗi.

Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin wanda ke wakiltar Mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim, ya bayyana cewa dukkan Kwamitocin Majalisar sun tattauna da Ma’aikatun Gwamnati da Hukumominsu kan tantancewa da kare ƙididdigar kasafin kuɗinsu.

Ya ce duba da abubuwan da kasafin ya ƙunsa, kwamitin ya gamsu da rabon kuɗaɗen da aka ware domin samar da ababen more rayuwa da walwalar al’umma a shekarar kasafin kuɗin 2026.

Dangane da kasafin kuɗin ƙananan hukumomi 27 da ya haura naira biliyan 288, Hamza Adamu ya yi kira ga Ma’aikatar Kananan Hukumomi da ta tabbatar cewa shugabannin ƙananan hukumomi suna bin aiwatar da kasafin kuɗinsu yadda ya dace domin jin daɗin al’ummar karkara.

A yayin zaman Kwamitin Majalisa gaba ɗaya (Committee of the Whole), Shugaban Majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya karɓa tare da duba shawarwari da gyare-gyare kan kura-kurai na rubutu musamman sunayen garuruwa da wurare.

Da aka koma zaman Majalisa na gaba ɗaya, Mataimakin Magatakardar Majalisa, Alhaji Yusha’u Muhammad, ya karanta kudirin dokar karo na biyu da na uku, inda Shugaban Majalisar, Haruna Aliyu Dangyatin, ya sanar da amincewa da Kudirin Dokar Kasafin Kuɗin shekarar 2026 ya zama doka.

Labarai

Labarai2 days ago

Gidauniyar NASARA Ta Raba Kayayyakin Ramadan da na Sallah ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Marayu da zawarawa sama da dubu ɗaya ne suka amfana da tallafin kayayyakin Ramadana da na Sallah...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Taiwo Oyedele Ministan Kudi

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Taiwo Oyedele a matsayin  Minista a Ma’aikatar. An gudanar...

Labarai2 days ago

Yi Wa Shuwagabanni Biyayya Ne Zai Kai mu Ga Ci Gaba – Garkuwan Kudun Zazzau

Dokta Muhammad Sani Uwaisu FCNA, Garkuwan Kudun Zazzau, ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmin Duniya baki daya da su...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Amince da Biyan Albashin Watan Maris Gabanin Bukukuwan Karamar Sallah

Daga Aminu Dalhatu Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma’aikatan gwamnati da...

Labarai2 days ago

Mambobin APC Sun Kai 158,697 a Zamfara Bayan Sauya Shekar Gwamna Lawal

Adadin mambobin jam’iyyar APC a jihar Zamfara ya karu zuwa 158,697, kwanaki uku kacal bayan sake bude tsarin rajistar mambobi...

Labarai2 days ago

Kwara NUJ Iftar: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Rika Tsayawa Kan Gaskiya

An bukaci ‘yan jarida su tabbatar rahotanninsu sun dogara da gaskiya tare da guje wa son zuciya domin kare mutuncinsu...

Labarai2 days ago

‘Yan Sanda Sun Bankado Maboyar Masu Garkuwa

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta samu wani gagarumin nasara a kokarinta na yaki da masu garkuwa da...

Labarai2 days ago

JIBWIS Ta Bukaci Gwamna Bago Ya Gaggauta Sanya Hannu Kan Dokar Hisbah

Shugaban Majalisar Malamai ta ƙasa na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Ash Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya...

Labarai5 days ago

An Yi Wa Jami’an FRSC A Jos Gwajin Idanu Kyauta Domin Ranar Glaucoma Ta Duniya

Jami’an kula da hanya na Hukumar Kiayyae hadura ta kasa a Jos sun samu damar yin gwajin idanu da kuma...

Labarai5 days ago

Kwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara

Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Jihar Kwara, ta ce ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta da kuma...

Mafi Shahara