Labarai
NLC Ta Gudanar da Gangamin Lumana a Kano
Daga Abdullahi Jalaluddeen
Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) ta gudanar da gangamin lumana a jihar Kano domin jawo hankalin jama’a kan ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasa, tare da miƙa wasikar bukatu ga Gwamnatin Jihar Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Suleiman Sani Wali, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin jihar na da kyakkyawar alaka da ƙungiyoyin ƙwadago, inda ya bayyana gangamin a matsayin shaida ta zaman lafiya da fahimta tsakanin gwamnati da ma’aikata.
Ya bayyana gamsuwarsa bisa yadda aka gudanar da gangamin cikin lumana da tsari, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da jajircewa wajen yin mu’amala mai kyau da ƙungiyoyin ƙwadago.
Shugaban Ma’aikatan ya tabbatar wa NLC cewa ana ɗaukar batutuwan tsaro da muhimmanci a jihar, inda ya ce dukkan hukumomin tsaro na aiki gwargwadon ƙarfinsu domin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a Kano.
Ya kuma ce gwamnan zai duba wasikar da NLC ta gabatar tare da tabbatar da cewa an isar da abubuwan da ke cikinta ga hukumomin da suka dace, ciki har da Shugaban Ƙasa.
Tun da fari, wakilin Shugaban NLC na ƙasa, Mista Muttaqa Yusha’u, ya ce gangamin ya yi daidai da kudurin Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na NLC na shirya gangamin lumana a fadin ƙasar domin wayar da kan jama’a kan matsalar rashin tsaro da kuma inganta zaman lafiya.
Yusha’u ya jaddada cewa rashin tsaro na shafar ma’aikata a kowane fanni, ciki har da malamai, ma’aikatan lafiya, manoma, ’yan kasuwa da jami’an tsaro, yana mai cewa ba za a samu ci gaba ba tare da tsaro da zaman lafiya ba.
Ya yi kira da a samar da tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi, tare da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin ma’aikata, domin shawo kan matsalolin tsaro yadda ya kamata.
Haka nan, Shugaban NLC na Jihar Kano, Mista Kabiru Inuwa, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a jiharjisai dai ya bukaci a ƙara ƙaimi domin hana yaɗuwar rashin tsaro daga sauran sassan ƙasar.
Inuwa ya jaddada buƙatar inganta walwala da tallafi ga jami’an tsaro da iyalansu, yana mai bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci da ƙungiyoyin ƙwadago shi ne hanya mafi dacewa ta samar da tsaro mai ɗorewa.
Kungiyar NLC ta sake jaddada aniyar ta na goyon bayan duk wata gwamnati da ke bada fifiko ga walwalar ma’aikata, zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
