Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Horas Da Yara Sana’o’i Tun Daga Matakin Firamare
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ta hanyar samar da tsari na ƙasa kan haɓaka sana’o’in hannu daban daban.
An bayyana hakan ne a taron Cibiyar Horas da Sana’o’i ta Kasa da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da Ministan Ilimi a matsayin mataimakinsa.
Bayan kammala taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa tattaunawar ta haifar da Ɗa mai ido, inda ya ce za a aika da kudirin kafa Cibiyar Horas da Sana’o’i ta Ƙasa zuwa majalisar dokoki nan ba da daɗewa ba.
Ya ce: “Manufar ita ce a daidaita ayyukan dukkan manyan masu ruwa da tsaki a wannan fanni. Kaduna ta riga ta amfana ƙwarai, inda Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da cibiyoyin koyon sana’o’i, inda dalibai sama 32,000 ke koyon sana’o’i daban daban.
Ministan Ilimi, Farfesa Tunji Alausa, ya jaddada cewa horar da sana’o’in hannu na kan gaba a cikin ajandar gwamnati, wacce ke daidai da alƙawarin Shugaba Tinubu na samar da damar ci gaba ga matasan Najeriya.
Ya bayyana cewa sabuwar manhajar ƙasa yanzu ta mai da hankali ne sosai kan fannoni na musamman guda shida, da suka hada da ɗinki, kiwon dabbobi, gyaran kwamfuta da wayoyin hannu, da sauransu, waɗanda su ne sana’o’in da kasa ke matukar bukata a yanzu.
Ita kuwa Minista a Ma’aikar Kwadago da Samar da Ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha, ta bayyana cewa Majalisar Zartaswa na kokarin tabbatar da cewa yara na samun horo kan sana’o’in hannu tun daga matakin farko na ilimi har zuwa girmansu.
Ta ce “Manufar ita ce a tabbatar kowanne yaro ya girma da wata kwarewa, don rage tarin matasan da ba su da aiki. Haku kuma kowa zai samu damar taka muhimmiyar rawa a cikin al’umma.”
Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
