Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Shirin Inganta Rayuwar Matasan Da Suka Tuba Daga Ayyukan Daba

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar Hukumar ’Yan Sanda ta Ƙasa sun kammala binciken  matasa 718 da suka daina harkar daba a ƙarƙashin shirin ‘Safe Corridor Project’ na jihar.

Wannan mataki muhimmin tsari ne na rage rashin tsaro da kuma bai wa matasa masu rauni damar zama nagari.

Bikin ƙaddamar da shirin ya gudana ne a ginin ‘yan sanda na officers’ mess da ke Bompai a Kano. A wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana shirin afuwar a matsayin dabarar zaman lafiya wajen magance laifuka da tashin hankali a jihar.

Gwamnan  wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Alhaji Ibrahim Waiya ya wakilta, ya bayyana cewa ƙarin matasa 960 da suka tuba na jiran tantancewa a mataki na gaba. Yana mai cewa an tsara shirin ne don kawo ƙarshen matsalolin tada-zaune-tsaye, satar waya da sauran laifuka, ta hanyar bai wa masu tuba damar gyara rayuwarsu don sake dawowa cikin al’umma, da kuma samun taimakon dogaro da kai.

Mun yi imanin cewa idan muka rungumi waɗannan matasa ta hanyar wannan dabarar zaman lafiya, za mu iya shawo kan ƙalubalen da muke fuskanta na fadan daba, wanda ya daɗe yana damun al’umma. Babban burinmu shi ne mu sa harkar daba ta zama tarihi a Kano.” In ji Gwamna Yusuf.

Ya ƙara da cewa za a yi wa matasan gwajin miyagun ƙwayoyi karkashin  shirin gyaran dabi’u na hukumar yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA. “Waɗanda suka tsallake wannan mataki za su samu tallafi daga gwamnati domin dogaro da kansu, don kauce wa komawa ga aikata laifi”. In ji shi.

A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba da ƙoƙarin gwamnati tare da tabbatar da aniyar hukumar ’yan sanda na ci gaba da tallafa wa shirin.

Ya jaddada cewa yaƙi da laifuka ba na ’yan sanda ba ne kaɗai, ya bukaci iyalai da al’umma su rungumi wannan aiki tare da hukumomin tsaro.

Shi ma Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris, ya bayyana goyon bayan hukumar ga shirin ‘Safe Corridor Project‘. Yana mai  cewa amfani da miyagun ƙwayoyi na daya daga cikin abubuwan da ke jefa matasa cikin tashin hankali, ya kuma jaddada muhimmancin ganin gwamnatin ta kara zage dantse domin samun zaman lafiya a jihar.

Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun shawarci matasan da su tsaya tsayin daka a kan tubansu, suna gargadin cewa kada su yi asarar wannan dama da gwamnati ta basu.

Su ma wasu daga cikin matasan da suka tuba da suka yi jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, sun gode wa gwamnati bisa wannan tsari, tare da yin alƙawarin zama ’yan ƙasa masu zaman lafiya da amfani a cikin al’umma.

 

Abdullahi Jalaluddeen

Labarai

Labarai7 hours ago

Hukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani

Ayyukan ban ruwa a yankin Kogin Benuwe na fuskantar barazana sakamakon taruwar Laka da Yashi a kogin, lamarin da ke...

Labarai1 day ago

Gwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu

Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya raba tallafin kayan abinci na watan Ramadan tare da...

Labarai1 day ago

Sojoji Sun Yi Nasarar Kwato Dabbobi 257 da Aka Sace a Karamar Hukumar Gwarzo

Daga Abdullahi Jalaluddeen Sojojin Najeriya sun sami nasarar dawo da Shanu da Awaki  257 da aka sata a  wani aikin...

Labarai1 day ago

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta Yaba da Yadda Aka yi Rabon Tallafin Ramadan

Daga Aminu Dalhatu  Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa...

Labarai1 day ago

Gwamnatin Kebbi Za ta Raba Hatsi da Kayayyakin Aikin Gona ga Marasa Galihu

Daga Sani Dutsinma Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen raba kayayyakin aikin noma da nau’o’in hatsi daban-daban ga mutane miliyan...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Kwara Ta Jaddada Kudurinta Na Kula Da Jin Daɗin Masu Harkar Sufuri

Gwamnatin Jihar Kwara ta bai wa masu harkar sufuri a jihar tabbacin ci gaba da kare muradunsu da jin daɗinsu....

Labarai2 days ago

Gwamnan Zamfara Ya Haramta Karbar Kudin Haraji A Hannu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umarnin dakatar da duk wani tsarin karbar kuɗaɗen shiga ta tsabar kuɗi...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Faɗaɗa Rijistar Tallafin Jama’a Domin Tantance Masu Buƙata

Gwamnatin Tarayya na faɗaɗa tare da ƙarfafa Rijistar Tallafin Jama’a ta Ƙasa National Social Register domin tabbatar da cewa an...

Labarai2 days ago

Gwamna Idris Ya Ba da Umarnin Binciken Gobarar da Ta Tashi a Makarantar Nurul Haqq da ke Birnin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar...

Labarai2 days ago

Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16

Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba ƙarƙashin Shirin IMPACT, ta ƙaddamar da rarraba kayan...

Mafi Shahara