Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Kayan Abinci Ga Al’ummar Najeriya

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara raba hatsi a faɗin ƙasar a wani mataki na rage matsin rayuwa da ƴan Najeriya suke ciki.

Ministan aikin gona Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a yau Litinin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Ina bai wa ƴan Najeriya da suke cikin halin matsin rayuwa haƙuri. Na san halin ƙunci da ake ciki, musamman ganin fasa rumbunan abinci da kuma wawaso da ake yi,” in ji ministan.

Ya ce yana son ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙari na ganin abubuwa sun daidaita.

Sanata Kyari ya ce shugaban ƙasa ya amince a fara raba Hatsi da ya kai tan dubu arba’in da biyu a faɗin jihohi 36 na ƙasar a wannan mako.

Muna aiki kafada da kafada da hukumar  bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da kuma jami’an tsaro na farin kaya DSS don tabbatar da cewa Hatsin ya kai hannun wadanda suka cancanta,  wato mabukata”.

Ministan ya ƙara da cewa za a fitar da tan dubu hamsin da takwas da dari biyar  na shinkafa zuwa kasuwanni a cikin farashi mai rahusa.

Har ila yau, ministan ya buƙaci ‘ƴan Najeriya da su ci gaba da mara wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu a kokari da take yi na ganin ta shawo kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Labarai

Labarai22 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara