Labarai
Majalisar Dokoki Ta Amince Da Kasafin Kudin 2025 Na Kananan Hukumomin Kaduna 23
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kasafin kudi na shekarar dubu biyu da ashirin da biyar na kananan hukumomi ashirin da uku a matsayin doka.
Shugaban Majalisar, Alhaji Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana cewa an kara kasafin kudin zuwa sama da naira biliyan dari da ashirin da uku.
Yayin gabatar da kudirin a zauren majalisa don amincewa, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi da Aiwatarwa, Yunusa Shehu Pambegua, ya bayyana cewa a baya bangaren zartaswa ya mika kasafin kudi na sama da naira biliyan dari da goma sha biyar na kananan hukumomi ashirin da uku na jihar.
Yunusa Shehu Pambegua ya bayyana cewa yayin kare kasafin kudinsu, shugabannin wasu kananan hukumomi sun nemi karin kudi don biyan bukatun ma’aikata da sauran kudaden gudanarwa.
Shugaban kwamitin ya ce bayan da shugabannin kananan hukumomi suka gabatar da yadda suka kashe kasafinsu kuma suka kare sabon kasafin, kwamitin ya gano cewa wasu kananan hukumomi suna bukatar gyara kasafinsu, kuma aka bukaci su rubuta hakan.
Ya ce an sake daidaita kasafin kudin tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa, inda sabon jimillar kasafin kudin ya karu zuwa sama da naira biliyan dari da ashirin da uku, ciki wanda kashe kudin yau da kullum ya kai kashi sittin cikin dari, yayin da na ayyukan ci gaba ya tsaya a kashi arba’in cikin dari.
Yunusa Shehu Pambegua ya shawarci shugabannin kananan hukumomi da su yi amfani da kasafin kudin yadda ya kamata ta hanyar gudanar da mulki na kowa da kowa don amfanin daukacin al’ummar Jihar Kaduna.
‘Yan majalisar sun amince da kudirin ba tare da sabani ba bayan ya tsallake karatu na uku, kuma yanzu ana jiran amincewar gwamna domin ya zama doka.
Cov/Shamsudeen Manir Atiku
-
Labarai5 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai3 days agoHukumar Kula da Kogin Benuwe ta Dauki Matakin Yashe Laka da Yashi da ke Barazana ga Noman Rani
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai7 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
-
Labarai5 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
