Labarai
Shugaban Majalisar Musulmi Ya Yi Kakkausar Suka Game Da Yadda Wasu Malamai Ke Sukar Junansu
Shugaban Majalisar Musulmi ta Kasa Ustaz Sadiq Abdulrahman Abiodun ya tunatar da malaman addinin musulunci bukatar yin amfani da hikima da kyautatawa yayin gabatar da wa’azi akan ka’idojin shari’ar musulunci domin sanya mabiyan su akan turbar da ta dace.
Shugaban ya sanar da hakan ne a taron bita ta yini guda da aka shiryawa malamai da limamam addinin musulunci a Kaduna.
Ustaz Sadiq Abdulrahman Abiodun ya nuna rashin jin dadin sa bisa yadda wasu malaman addinin musulunci ke amfani da kafafen sada zumunta na zamani suna sukar junan su, wanda a cewar sa wannan bai dace da tsarin addinin musulunci ba, maimakon haka su yi amfani da kafafen wajen yada addinin musulunci.
Shugaban ya ce ya zama wajibi ga Majalisar Kula da Addinin Musulunci ta Kasa ta janyo hankalin malamai su shiga taitayinsu, a matsayinsu na masu dora mutane akan tafarkin bautawa Mahalicci sannan su gudanar da tsaftatacciyar rayuwa.
Ya yi kira ga iyaye musulmi su rika duba takardu da darussan da ake koyawa ‘ya’yansu a makarantu don gudun ka da a koya musu munanan dabi’u da ka iya bata musu tarbiya.
Da yake gabatar da makala akan muhimmancin ilimi ga rayuwar malaman addinin musulunci, limamin masallacin MCAN a Kabala da Unguwan Mu’azu, Alfa Abdulrasheed Muhammed Jami’u Al-Iraqi, ya ce ya zama wajibi malaman addinin musulunci su zurfafa neman ilimin addini domin ilmantar da mabiya dokokin shari’ar musulunci sau da kafa a kasar nan.
Ya shawarce su da kada su nuna son rai da jahiltar fannin da basu da kwarewa akai, don gudun kada su yada karya akan addinin musulunci, wanda yin hakan ka iya batar da mutane.
Shi ma a makalar da ya gabatar mai taken, Dabarun Gabatar da Wa’azi, wanda malamai ya kamata su rika amfani da su, Alfa Ahmed Busairy ya ce ya zama wajibi malaman addinin musulunci su lakanci ilimin nahawu, baya ga sanin Qur’ani da Sunnah.
Ya kara da cewa, akwai bukatar malaman addinin musulunci su yi amfani da hikima da nuna juriya da hakuri yayin gabatar da wa’azi, kasancewar suna mu’amula da mutane masu sabanin fahimta.
Taron bitar na yini guda ya samu halartar malami da Limaman addinin musulunci daga kungiyoyin musulunci da dama.
Shamsuddeen Munir Atiku
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
