Wasanni
Kwantaragin Kocin Super Eagles Na Najeriya Ta Kare
Kocin Najeriya Jose Peseiro ya sanar da kammala aikinsa da tawagar Super Eagles.
Kocin ɗan asalin Portugal ya bayyana hakan ne a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a ranar Juma’a.
“A jiya muka kawo ƙarshen kwantaragin da ake tsakanina da Hukumar Kwallon ƙafa ta Najeriya NFF.”
“Abin farinciki da alfahari ne koyar da tawagar Super Eagles. Watanni 22 kenan da muka kwashe muna wannan sadaukarwa da mutakuar sha’awar aikin. Muna jin mun yi abin da ya kamata,” kamar yadda kocin ya rubuta.
Ya ce yana so ya nuna godiyarsa ga tsohon shugaban hukumar NFF Amaju Pinnick da kuma na yanzu Ibrahim Gusau da Sakataren NFF Mohammed Sanusi da duka ma’aikatan hukumar da duka ‘yan wasan, wadanda duka muka yi zaman kirki da su.
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai50 minutes agoAKCILS Ta Karrama Jami’in Tsaro Bayan Shekaru 22
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
