Connect with us

Labarai

Gwamnatin Neja Ta Haramtawa Motocin Da Suka Fito Daga Hanyar Maje Bin Gadar Dikko

Published

on

Gwamnatin Jihar Neja ta ba da umarnin hana motocin da suka  fito daga Maje hawa gadar Dikko.

Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya ba da umarnin a lokacin da ya ziyarci wurin da wata tankar mai  ta yi  gobara a mahadar Dikko da ke karamar hukumar Gurara ta jihar Neja.

Gwamnan, wanda ya koka kan yadda wasu direbobi ke nuna halin ko-in-kula yayin tuki, ya ce ba a amince duk wata mota da ta fito daga Maje ta bi ta gadar Dikko ba, sai dai su bi karkashin gadar zagayo kan hanyarsu.

Ya kuma umurci babban kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya da ya kafa rundunar tsaro a yankin domin tabbatar da aiwatar da wannan umarni, yayin da ya yi kira ga kungiyoyin sufuri da abin ya shafa da su ba hukumar kiyaye hadurra ta kasa hadin kai.

Sai dai Gwamnan ya bayyana fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a matsayin abin tausayi tare da gode wa Allah da lamarin bai kai ga al’ummar da ke makwabtaka da su ba.

Umar Bago ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar matakin kammala aikin titin Minna zuwa Suleja domin jinkirin aikin hanyar yana haddasa asarar  rayuka da dukiyoyi.

Gwamnan ya godewa Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, da Hukumar Kashe Gobara, da Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, da Kungiyar Sufuri ta Kasa (NURT) da sauran hukumomin da suka bayar da gudunmawa wajen kawo dauki ga  wadanda fashewartankarya rutsa da su.

Ya ce za a kara  tura likitoci daga asibitocin da ke Minna domin su taimaka wajen kula da wadanda suka jikkata da ke samun kulawa a  babban asibitin Suleja.

Daga Aliyu Lawal

Labarai

Labarai24 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara