Connect with us

Labarai

Wadanda Iftila’in Tankar Mai Ya Sha A Jigawa Sun Sami Naira Miliyan 4 Kowannensu

Published

on

Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia.

Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu.

Kamar yadda aka bayyana a ranar Laraba 26 ga watan Maris 2025, jimillar kuɗin da aka tattara sun kai Naira miliyan 839. Bisa ga kididdiga da aka yi, kowanne daga cikin mutanen da lamarin ya shafa kai tsaye zai karɓi kimanin Naira miliyan huɗu.

“Ga waɗanda suka rasu, za a ba da kuɗin ga iyayensu ko magadansu, yayin da waɗanda suka tsira za su karɓi nasu da kansu.

“Kayan tallafin da aka riga aka tara, musamman abinci da sauran kayayyakin bukata, tuni an raba su ga waɗanda suka shafi lamarin“, in ji shi.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa akalla mutane 210 ne lamarin ya ritsa da su, inda 100 daga cikinsu suka mutu nan take.

An tabbatar da cewa mutane 33 daga cikin waɗanda suka rasu magidanta ne, kuma 31 daga cikinsu sun bar ‘yaya. Jimillar matan da suka rasa mazajensu sakamakon lamarin sun kai 42, yayin da yaran da suka zama marayu suka kai 133″, in ji Gwamna Namadi.

A yayin jajantawa ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamnan ya yi kira ga direbobin manyan motocin dakon mai da sauran masu amfani da tituna su kasance masu taka tsantsan domin gujewa sake afkuwar irin wannan mummunan lamari.

Iftila’in da ya afku a Majia ya koyar da mu darussa masu yawa, wanda muke fatan jama’a da masu ruwa da tsaki, musamman ma waɗanda ke harkar sufuri, za su dauki darasi“. Inji shi.

Gwamnan ya kuma shawarci waɗanda suka karɓi tallafin su yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, musamman wajen kafa sana’o’i.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara