Fasaha
Sabuwar jami’ar Ilorin ta yaye dalibai karon farko su 146.
Sabuwar jami’ar Muhammad Kamaludeen dake Ilorin ta yaye dalibai karon farko da suka su 146.
Da yake nasa jawabin shugaban jami’ar Farfesa Rasheed Jimoh ya bayyana cewa jami’ar ta bullo da wani kwas na zamani wanda zai baiwa sabbin dalibai sama da Dala dubu 1000 domin yiwa kamfanonin da suke son yi rijista domin bunkasa sana’o’insu.
Ya ce jami’ar ta bullo da wasu tsare-tsare da za su baiwa daliban damar yin tunani mai zurfi don ba su damar gogayya da sauran kamfanonin kasashen duniya.
Shugaban jami’ar ya bayyana cewa daya daga cikin irin wadannan tsare-tsare shi ne samar da sabbin kwasa-kwasai da samar da ra’ayoyi don baiwa dalibai tun daga zangon karatunsu na farko da sana’o’in da suka dace da kuma sabbin dabaru .
Farfesa Jimoh ya lura cewa jami’ar za ta sauƙaƙe rajistar kamfanonin ta hanyar Hukumar yiwa kamfanoni rijista (CAC) da kuma taimaka wa don haɓaka ta hanyar saka hannun jari a kamfanonin.
Ya ce jami’ar dai tana da kwasa-kwasai 15 da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta amince da su.
A nasa jawabin, Uban jami’ar kuma Mai Martaba Sarkin Ilọrin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya bukaci masu neman shiga jami’a da su yi amfani da irin kwasa-kwasan da sabuwar jami’ar ta ke da su.
Mai martaba Sarkin ya mika godiyarsa ga wanda ya assasa kungiyar Ansarul Islam Society of Nigeria, Marigayi Sheikh Muhammad Kamaldeen Al- Adabbiy bisa hada ilimin addinin musulunci da ilimin zamani wanda a karshe ya kai ga kafa jami’a a tunawa da shi.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
