Labarai
Wani Fasinja Ya Yi Kashin Sama Da Dauri 100 Na Hodar Ibilis- NDLEA
Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce yanzu haka ta na rike da wani fasinjan jirgin saman dake kan hanyar zuwa birnin Paris ta kasar Faransa saboda zargin mallakar hodar ibilis, inda ya yi kashin dauri dari daya da goma sha daya na hodar da ya hadiye a cikinsa bayan an kama shi.
Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi yace sun kama wannan mutumin mai suna Emmanuel Okechukwu Orjinze ne a tashar jiragen saman Abuja lokacin da yake kokarin tsallake wuraren binciken fasinjoji domin hawa jirgin sama.
Okechukwu ya shaidawa NDLEA cewar shi ‘dan kwallo ne a Turai lokacin da aka kama shi a ranar 21 ga wannan wata a daidai lokacin da yake kokarin hawa jirgin Air France mai lamba 878 dake shirin barin Abuja zuwa Paris.

Bayan gudanar da bincike a kansa da na’ura, an tabbatar da cewar akwai tarin kunshin hodar ibilis wato cocaine a cikin sa, abin da ya sa aka tsare shi na tsawon kwanaki 3 kuma aka yi sa’ar ganin ya yi kashin wadannan dauri 111 da nauyin su ya kai kilo 1,603.
Yanzu dai haka Okechukwu na can a tsare inda ake sa ran gabatar da shi a gaban kotu domin amsa tambayoyin hukumomin shari’a.
Babafemi ya kuma bayyana nasarar da hukumar NDLEA ta samu na tarwatsa wata kungiya ta masu hadahadar miyagun kwayoyi a tashar jiragen saman Lagos, tare da kama mutane 4 daga cikin su da kuma kwace kilo 8 na hodar methamphetamine da kilo 7 da rabi na kwayar da ake kira cloud da ake safarar ta daga kasar Afirka ta kudu.
Jami’in yace ya yin gudanar da bincike, an kuma kama wasu karin mutane 2 a unguwar rukunin gidajen dake Ajao Estate dake birnin na Lagos.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
