Ilimi
Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Dr. Muheeba Dankaka a matsayin shugaban hukumar kula da da’a ta tarayya (FCC) a wa’adi na biyu na shekaru biyar.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce nadin na daya daga cikin alkawurran da shugaban kasar ya yi na “karfafa hukumar don tabbatar da adalci, daidaito da kuma hada kai a nade-naden na tarayya bisa tanadin tsarin mulki.”
Shugaban ya kuma nada Mohammed Musa a matsayin sakataren hukumar sannan Kayode Oladele daga jihar Ogun a matsayin kwamishina. An nada Oladele, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne a hukumar a shekarar 2024 kuma ya rike mukamin shugaban riko bayan kammala wa’adin farko na Dankaka.
Sauran kwamishinonin da suka dawo sun hada da Lawal Ya’u Roni (Jigawa), Abubakar Atiku Bunu (Kebbi), da Eludayo Eluyemi (Osun).
Sabbin kwamishinonin da aka nada sune:
- Hon. Obina Oriaku (Abia)
- Mrs. Bema Olvadi Madayi (Adamawa)
- Obongawan Dora Ebong (Akwa Ibom)
- Hon. Nnoli Nkechi Gloria (Anambra)
- Babangida Adamu Gwana (Bauchi)
- Sir Tonye Okio (Bayelsa)
- Aligba Eugene Tarkende (Benue)
- Engr. Modu Mustapha (Borno)
- Dr. Stella Odey Ekpo (Cross River)
- Edrin Lovette Idisi (Delta)
- Barr. Nwokpor Vincent Nduka (Ebonyi)
- Hon. Chief Victor Sabor Edoror (Edo)
- Hon. Sola Fokanle (Ekiti)
- Peter Eze (Enugu)
- Ibrahim Baba Mairiga (Gombe)
- Hon. Jerry Alagbaoso (Imo)
- Ruth Jumai Ango (Kaduna)
- Muhammad Awwal Nayya (Kano)
- Hon. Anas Isah (Katsina)
- Bello Idris Eeye (Kogi)
- Dr. Ibrahim Abdullahi (Kwara)
- Alh. Isah Jibrin (Niger)
- Comrade Ajimudu Bola (Ondo)
- Prince Ayodeji Abas Aleshinloye (Oyo)
- Hon. Pam Bolman (Plateau)
- Haruna Chukwuemeka (Rivers)
- Alh. Aminu Tambar (Sokoto)
- Comrade Bobboi Bala Kaigama (Taraba)
- Hon. Jibir Maigari (Yobe)
- Sani Garba (Zamfara)
- Solomon Ayuba Dagami (FCT)
PR/BELLO WAKIL
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
