Labarai
Gwamna Namadi Ya Rantsar da Sabbin Masu Bashi Shawara na Musamman Su 3
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rantsar da sabbin masu bashi na musamman guda uku da aka naɗa, a zauren majalisar zartarwa na fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar ga manema labarai, ya ce waɗanda aka rantsar su ne Alhaji Kabiru Hassan Sugungum, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Ƙasa; Ibrahim Ahmad Kwaimawa, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Dangantakar Masana’antu; da Ado Sani Birnin Kudu, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Ma’aikatan Gwamnati.

Yayin da yake rantsar da su, Gwamna Namadi ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin lokaci na ƙarfafa gwamnatinsa da kuma bunƙasa jihar.
A cewarsa, an zaɓi waɗanda aka naɗa ne bisa cancanta, gaskiya, ƙwarewa da kuma tabbacin iya ba da gudummawa mai ma’ana wajen aiwatar da shirye-shirye da manufofin gwamnati.

Gwamna Namadi ya tunatar da su cewa hidimar jama’a amana ce, inda ya jaddada cewa rantsuwar da suka yi tana nuni da alkawari mai girma a gaban Allah da al’ummar Jihar Jigawa.
“Yayin da nake taya ku murna kan kai wa wannan mataki, yana da muhimmanci a tunatar da ku nauyin da ke tare da wannan mukami. Hidimar jama’a amana ce, kuma rantsuwar da kuka yi a yau alkawari ne mai a gaban Allah da al’ummar Jihar Jigawa. A duk lokacin da ake irin wannan taro, nakan ji nauyin jagoranci sosai domin shugabanci daukaka ce kuma babban nauyi ne,” in ji Gwamnan.

Ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu da gaskiya, jajircewa da tawali’u, tare da fifita muradun jihar a kan komai.
Gwamnan ya kuma shawarce su da su ci gaba da ba da gudummawarsu wajen yi wa jihar hidima, kamar yadda suka saba yi a tsawon shekaru.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa da kyakkyawar niyya da jajircewa, Allah zai musu jagoranci tare da su taimaka musu wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
Da yake mayar da martani a madadin sauran abokan aikinsa, Mai bada shawara na Musamman kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Alhaji Kabiru Hassan Sugungum, ya nuna matuƙar godiya ga Gwamna bisa amincewar da ya nuna musu.
Ya tabbatar wa Gwamnan da cikakkiyar biyayyarsu ga gwamnatinsa da Majalisar Zartarwar Jihar, tare da alƙawarin bayar da gudummawa yadda ya kamata wajen nasarar aiwatar da Ajanda 12 na Gwamna Namadi, daidai da Ajandar Sabunta kudurori ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Alhaji Sugungum ya ce nauyin da aka ɗora musu ne ya ƙara musu karsashi, kuma da yardar Allah za su yi aiki tukuru domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, tare da tallafa wa hangen nesa na Gwamna na ganin Jigawa ta kara samun ci gaba.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
