Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro

Published

on

Daga Bello Wakili

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.

A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.

Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025.

An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da matsakaitan Sojoji (NDA) duk dai a wannan shekarar, inda ya samu digiri na daya a fannin kimiyya a 1991.

An daga Janar Musa zuwa matsayin babban Laftanar  (Second Lieutenant) a 1991, kuma tun daga lokacin ya yi aiki a manyan mukamai iri-iri. Daga cikin mukamansa akwai: Babban Jami’in Ma’aikata a bangaren Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81;
Kwamandan Bataliya ta 73;
Mataimakin Darakta, Kayayyakin Aiki, Sashen Tsare-tsaren Rundunar Soja;
Wakilin Sojin Kasa a Kwamitin Horaswa na Hedikwatar Soji ta Najeriya.

A 2019, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Babban Jami’in Ma’aikata na Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Cibiyar Sojin Kasa;
Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Lafiya Dole; da kuma Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Yankin Tafkin Chadi (Multinational Joint Task Force).

A 2021, an nada shi Kwamandan  Operation Hadin Kai, inda daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, kafin daga bisani Shugaba Tinubu ya nada shi Shugaban Hafsoshin Tsaro a 2023.

A cikin wasikar da ya aikewa Majalisar Dattawa, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken kwarin gwiwa kan ƙwarewar Janar Musa wajen jagorantar Ma’aikatar Tsaro tare da ƙara inganta tsarin tsaron Najeriya.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara