Labarai
Ruwan Wutan sojan Nijeriya Ya Kashe ‘Yan Bindiga A Zamfara.
Dakarun Operation FANSAN Yamma (OPFY) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a wani hari da suka kai ta sama da kasa a yankin Makakkari da ke dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.
Wannan farmakin wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2025, ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa dimbin ‘yan ta’addan da ke biyayya ga marigayi Halilu Buzu da Alhaji Beti sun taru a cikin dajin inda suka shirya kai harin ramuwar gayya kan al’ummomin Addabka da Nasarawan Burkullu a garin Bukkuyum.
Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Fansan Yamma OPFY’ Kyaftin David Adewusi, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa, harin da suka shirya kai harin shi ne ramuwar gayya da suka sha a baya-bayan nan a arangamar da suka yi da jami’an tsaro da wasu rundunonin tsaro.
Ya bayyana cewa, a wani samame na hadin gwiwa na kasa da ya biyo baya, dakarun da ke karkashin sashe na 2 sun kame tare da fatattakar ‘yan ta’addan da suka gudu daga inda aka kai harin ta sama.
Kyaftin Adewusi ya tabbatar wa ‘yan kasa masu bin doka da oda cewa ‘yan ta’adda da sauran masu rike da makamai ba za su samu mafaka a yankin Arewa maso Yamma da wasu sassan shiyyar Arewa ta tsakiya ba.
Ya nanata kudurin sojojin na fatattakar abokan gaba a duk inda suka taru ko kuma suka matsa sannan ya bukaci mazauna yankin da su baiwa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar ba da rahoton abubuwa, yana mai cewa bayanan da suka dace kan lokaci na da matukar muhimmanci wajen kare al’umma da kuma kawo karshen barazanar ta’addanci da ‘yan fashi.
REL/AMINU DALHATU.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
