Labarai
NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido daga Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON domin tantance ayyukan hukumar.
A jawabin shugabar tawagar kuma babbar jami’ar hukumar ta NAHCON a jihar Jigawa Hajiya Rabi’atu Dahiru Nyako, ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce tantance kayayyakin aikin hukumar tare da duba yaddatake gudanarda shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
“Tawagar za ta tantance kayan aiki, da shirye-shiryen jigilar maniyyatan jihar, da takardun tafiya kasa mai tsarki, da fasfo fasfo da sauransu”.
Babbar Jami’iar ta bayyana gamsuwa da irin shirye-shiryen da hukumar ta yi.

A nasa jawabin, babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, an samu nasarori da dama a kan shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2024 a jihar.
Shugaban hukumar ya kara da cewa, hukumar ta kara wa’adin gudanar da lakcocin aikin hajji ga maniyyatan da ke fadin kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar.
Ya nanata kudurin gwamnatin jihar na tabbatar da jin dadin Alhazan Jigawa tun daga gida Najeriya har zuwa kasar Saudiyya.

Labbo ya yabawa NAHCON bisa ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga hukumar domin samun nasarar aikin Hajjin na bana.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tawagar ta duba sashin amfani da na’ura mai kwakwalwa, da ayyukan da ake gudanarwa, tare da wasu gine-gine da aka gyara, da sauran kayayyakin zamani na hukumar.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai7 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai1 day agoGwamna Namadi Ya Raba Tallafin Ramadan ga Ma’aikata da Marasa Galihu
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
