Labarai
Karamar Hukumar Miga Ta Yi Wa Tsara Zarar Wajen Fatar da Zakkar Amfanin Gona
Daga Usman Muhammad Zaria
Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Muhammadu Nuhu Sanusi ya kaddamar da rabon zakkar kayayyakin amfanin gona ta shekarar musulunci ta 1447 a gundumar Miga dake Jihar Jigawa.
A lokacin da yake jawabi, Mai Martaban ya bayyana cewar an kaddamar da rabon zakkar ne a Miga kasancewarta ta farko wajen tattara zakkar amfanin gona a shekarar 2025.

A don haka, Alhaji Hamim Muhammadu Sunusi, ya hori al’ummar Miga da su kasance masu son zaman lafiya da junan su gami da gujewa tada fitina.

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Miga, Mallam Bilya Garba ya bada tabbacin ci gaba da marawa gundumar baya domin rike kanbunta wajen tattara zakka.

Tun da farko a jawaninsa, Sa’in Dutse Mallam Mahmud Yunusa ya yi bayani dalla dalla kan yawan zakkar da kowacce gunduma ta samu.

Wakilinmu ya bamu rahoton cewar, an tara zakar amfanin gona ta naira miliyan 623 da dubu 822 a shekarar 2025.

Amfanin gonan sun hada da Dammunan Gero da Dawa 40, 558 da kuma bahunan gero da Dawa 2,181 da za a rabawa mabukata har su 29,906.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
