Labarai
Hukumar Kwastam Ta Inganta Shirye-shiryen AfCFTA Kafin Taron Abuja
Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce tana ƙara ƙoƙari wajen aiwatar da cikakken tsarin Yarjejeniyar Cinikayya ta Nahiyar Afrika (AfCFTA), yayin da kasar ke shirin karɓar babban taron cinikayyar nahiyar a Abuja.
Babban Kwanturolan Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana haka yayin da yake wa manema labarai jawabi a Fadar Shugaban Kasa kan shirye-shiryen Hukumar na karɓar taron Partnerships for African Customs and Trade (PACT).
Gwamnatin yanzu ta bayyana a fili cewa za ta yi amfani da cinikayya wajen inganta tattalin arziki da rage talauci.
Babban Kwanturolan ya kara da cewa sabon wa’adin da Shugaba ya ba shi ya ƙunshi aiwatar da Yarjejeniyar Cinikayya ta Nahiyar Afrika a matsayin muhimmin ma’aunin ayyukansa.
Ya ce manufar gwamnati ta haɗa da rage cunkoson tashoshin jiragen ruwa, zuba jari a muhimman kayan aikin tashoshi, da kuma amfani da sabbin fasahohi irin su single window domin saukaka cinikayya.
Shugaban Kwastam ya bayyana cewa ya gudanar da muhimman tattaunawa da shugabannin kwastam daga kasashen Afrika da ma’aikatar AfCFTA domin tabbatar da cewa hukumomin kwastam sun shiga tsakani sosai a tattaunawar aiwatar da yarjejeniyar.
Ya jaddada cewa kwastam na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ka’idojin asalin kaya, bayar da rangwamen haraji, da kuma rage kudaden kwastam a hankali har su zuwa sifili tsakanin kasashen Afrika.
Adeniyi ya kuma bayyana kalubalen da ake fuskanta a shirin haɗin gwiwar tattalin arzikin yankin ECOWAS, musamman a tsarin ECOWAS Trade Liberalization Scheme, inda kasashe da dama suka kasa cika ka’idoji.
Ya ce wannan ne ya sa ake ƙara zurfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin kwastam, masu gudanar da harkokin kasuwanci, da sauran hukumomin da ke da alhakin kula da cinikayyar ketare.
Yayin da aka nada Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin Jagoran Cinikayyar Cikin Nahiyar Afrika, kuma Najeriya aka zaɓa ta karɓi baje kolin cinikayyar cikin nahiyar na gaba (Intra-African Trade Fair), Adeniyi ya ce hukumomi da dama irin su Hukumar Ƙarfafa Fitar da Kaya ta Najeriya (NEPC) da NEXIM Bank suna aiki tare wajen karkatar da kasuwancin Najeriya zuwa kasashen Afrika.
Ya tabbatar da cewa kasashen kwastam fiye da 30 daga Afrika sun yi rijista domin halartar taron, da yawancin su a matakin Darakta Janar. Kamfanoni masu zaman kansu—ciki har da masu jigilar kayayyaki, kamfanonin jiragen sama, masana’antu, da kamfanonin sufuri—su ne mafi rinjaye a cikin mahalarta.
Adeniyi ya ce za a fara taron ne da zaman musamman tare da ‘yan kasuwa masu zaman kansu domin jin kai tsaye matsalolin da suke fuskanta, ciki har da shingayen da ba na haraji ba (non-tariff barriers) da ke kawo tsaiko a cinikayyar nahiyar.
A kan batun kudaden shiga, Babban Kwanturolan ya ce ko da yake haraji na da muhimmanci, Hukumar ta karfafa sauran nauyin aikinta—tsaron kasa da saukaka cinikayya—ta hanyar amfani da sabbin kayan aiki da tsarin zamani. Wadannan abubuwa, a cewarsa, sun taimaka wajen kama muggan miyagun ƙwayoyi, makamai, da harsasai, tare da ƙaruwa sosai a kudaden shiga: kashi 70 cikin ɗari a shekarar 2023 da kuma kashi 101 cikin ɗari a 2024.
Ya kara da cewa Hukumar ta kusa sake zarce nasarorin kudaden shiga na shekarar 2025.
BELLO WAKILI
-
Labarai2 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
