Connect with us

Labarai

Jigawa Ta Kulla Yarjejeniya da Cibiyar AfricaRice Don Inganta Noman Shinkafa

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria 

Gwamna Umar Namadi ya kulla yarjejeniya da Cibiyar Binciken Shinkafa ta Afrika (AfricaRice) domin hanzarta bunkasa noman shinkafa da karfafa samar da abinci a jihar Jigawa.

An rattaba hannu kan takardar yarjejeniyar ne yayin wani babban taro da aka gudanar a Bouaké na kasar Côte d’Ivoire.

Daraktan Hukumar Sauya Fasalin Aikin Noma ta Jigawa (JATA), Dr. Saifullahi Umar, da Daraktan AfricaRice, Dr. Baboucarr Manneh, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

A lokacin bikin rattaba hannun, Gwamna Namadi ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na gina tsarin noman shinkafa na zamani a jihar.

Wannan hadin gwiwa da AfricaRice shaida ce ta jajircewarmu wajen farfado da harkar noma da bunkasar tattalin arziki. Mun kuduri aniyar samar wa manomanmu kayan aiki da ilimi da za su tabbatar da Jigawa ta zama cibiyar noman shinkafa,” in ji shi.

Daraktan JATA, Dr. Saifullahi Umar, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin matakin sauyi mai ma’ana ga fannin noma a Jigawa, yana mai cewa hakan zai  hanzarta canjin jihar zuwa noma na zamani.

Shi ma Daraktan AfricaRice, Dr. Manneh, ya bayyana shirinsu na tallafawa burin jihar ta Jigawa  yana cewa cibiyar za ta gabatar da sabbin dabaru da za su inganta noman shinkafa a matakin kasa.

Hadin gwiwar zai fara ne da zaman tsare-tsare don fitar da muhimman ayyuka da kuma kaddamar da gwaje-gwajen gona a yankunan dabi’un noma daban-daban na jihar.

AfricaRice, wacce aka kafa a 1971 kuma ke da hedikwata a babban birnin Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, kungiya ce ta bincike mai yunkurin rage talauci da karfafa samar da abinci a Afrika, ta hanyar ingantaccen bincike kan shinkafa da karfafa hadin gwiwa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara