Labarai
Hajjin 2026: Jigawa ta Fara Tantance Lafiyar Maniyyata
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa maniyyata masu cikakkiyar lafiya ne kadai za a lamincewa zuwa aikin Hajjin 2026.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan a Babban Asibitin Gwamnati na Hadejia yayin ƙaddamar da shirin tantance lafiyar maniyyata aikin Hajjin 2026 a hukumance.

Ya ƙara da cewa shirin na daga cikin shirye-shiryen da hukumar ke yi domin tabbatar da lafiyar Alhazan jihar.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada cewa hukumar ta jajirce wajen bin ƙa’idojin Saudiyya, waɗanda suka tanadi cewa mutanen da ke da cikakkiyar lafiya ne kaɗai za su gudanar da aikin Hajjin.

Ya kuma bayyana cewa za a gudanar da tantancewar cikin adalci da gaskiya domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Wasu daga cikin maniyyatan sun yabawa hukumar bisa yadda take gudanar da shirin.
Rediyon Nijeriya ya ruwaito cewa Darakta Janar ɗin ya samu rakiyar Daraktan Ayyuka, Alhaji Muhammad Garba.
-
Labarai3 days agoAdalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazan Jihar Jigawa ta Kaddamar da Kwamitin Amirul Hajjin Bana
-
Labarai2 days agoRadio Nigeria @75: Tsohon Dan Jarida Ya Yi Waiwaye Kan Tarihi Radio Nijeriya
-
Labarai7 days agoTrump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran
-
Labarai2 days agoMasarautar Saminaka ta Bukaci Hadin Kai Don Dorewar Zaman Lafiya a Yankin
-
Labarai2 days agoHukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta Kammala Shirin Rigakafi ga Maniyyatan Bana
-
Labarai5 days agoHajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
-
Labarai2 days agoƊaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Huɗu Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano
